Al’ummar Musulmi a Masarautar Kaltungo sun gudanar da Sallar Idi ta Eid-el-Kabir tare da bukukuwan Hawan Sallah. Babban Limamin Kaltungo, Liman Muhammad, ya yi kira ga Musulmi su ci gaba da riko da tsoron Allah, ayyukan alheri da taimakon marasa galihu. Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad, ya bukaci al’umma su zauna lafiya tare da karfafa hadin kai tsakanin manoma da makiyaya, sannan ya yi kira ga shugabanni su kara himma wajen samar da abubuwan more rayuwa a karkara. Bukukuwan sun samu halartar masu sarautun gargajiya, kungiyoyin al’adu da dimbin jama’a.
Culture
Masarautar Kaltungo Ta Yi Kira ga Zaman Lafiya Yayin Bukukuwan Eid-el-Kabir
Masarautar Kaltungo ta yi kira ga zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna yayin bukukuwan Eid-el-Kabir. Kiran na kunshe ne a sakonnin da Babban Limamin Kaltungo da Mai Kaltungo suka gabatar a lokacin Sallar Idi da Hawan Sallah.