Wata sanarwa da mai taimaka wa dan takarar kan harkokin yada labarai, Ibrahim Sani Shawai ya fitar ta ce an kaddamar da kungiyar ne a karshen mako tare da halartar wakilai daga mazabun kananan hukumomi dana matakin jiha. Sanarwar ta ambato Mai Kula da Kungiyar a Jihar Gombe, Ibrahim Umar Babangida, na cewa an kafa kungiyar ne domin karfafa gwiwar magoya bayan jam’iyyar APC da kuma fadada ayyukan siyasa daga tushe a fadin jihar. Ya ce kungiyar na da burin isar da sako ga dukkan rumfunan zabe 2,988 da ke jihar Gombe domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC da ’yan takararta a zabukan da ke tafe. Haka kuma sanarwar ta ambato Dakta Jamil Isyaku Gwamna yana gode wa mambobin kungiyar bisa goyon baya da jajircewar da suka nuna a tafiyarsa ta siyasa. A cewarsa, irin hadin kai da kuma shirye-shiryen da ake gani a fadin kananan hukumomin jihar na kara masa kwarin gwiwa kan makomar jam’iyyar. Dakta Gwamna ya kuma sake jaddada goyon bayansa ga kungiyar tare da kira ga mambobinta da su ci gaba da aiki tukuru domin karfafa APC daga matakin tushe zuwa sama. Sanarwar ta bayyana taron a matsayin irinsa na farko tun bayan da Dakta Jamil Isyaku Gwamna ya samu tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Gombe. Sanarwar mai dauke dasa hannun Ibrahim Sani Shawai, mai taimaka wa dan takarar gwamnan APC a jihar Gombe kan harkokin yada labarai.
Politics
Dan Takarar Gwamnan APC a Gombe Ya Kaddamar da Kungiyar Jamilu Renewed Hope Movement
Dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC, Dakta Jamil Isyaku Gwamna, ya kaddamar da kungiyar Jamilu Renewed Hope Movement domin kara karfafa wayar da kan magoya baya da kuma shirye-shiryen tunkarar zaben shekarar 2027.