Government

SHIRIN TALLAFA WA MATA NA NAJERIYA: HAJIYA HAUWA ADAMU SARIKI TA YI BAYANI KAN YADDA AKE CIN GAJIYARSA

Kamal Hammajo Adam Sunday, 14 June 2026 15 views

Hajiya Hauwa Adamu Sariki, Mai Kula da Ayyukan Shirin Tallafa wa Mata na Najeriya (Nigeria for Women Programme Scale-Up Project) a Jihar Gombe, ta yi bayani kan manufar shirin da kuma hanyoyin da mata za su bi domin cin gajiyar damar da yake samarwa.

Mai Kula da Ayyukan Shirin Tallafa wa Mata na Najeriya (Nigeria for Women Programme Scale-Up Project) a Jihar Gombe, Hajiya Hauwa Adamu Sariki, ta yi cikakken bayani kan manufofi da ayyukan shirin, tare da bayyana yadda mata za su iya cin gajiyar damar da shirin ke samarwa. A yayin hirarta da Nexus Channels, Hajiya Hauwa Adamu Sariki ta bayyana cewa shirin na da nufin ƙarfafa tattalin arzikin mata, inganta rayuwarsu da kuma samar musu da hanyoyin dogaro da kai ta hanyar haɗa su cikin ƙungiyoyi, ba su horo da kuma sauƙaƙa musu samun tallafi da sauran damammaki. Ta kuma yi kira ga mata a faɗin Jihar Gombe da su rungumi shirin domin cin moriyar damammakin da yake samarwa, tana mai jaddada cewa shirin zai taimaka wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da inganta walwalar iyalai da al’umma baki ɗaya. Ku kalli cikakkiyar hirar domin jin ƙarin bayani kan yadda za a amfana da wannan shiri.


Related News
Gombe Chief Judge Urges Digitalisation of Judiciary
Read More
Northern Governors, Traditional Rulers Back State Police, Renew Regional Security Push
Read More
Northern Governors, Traditional Rulers Back State Police, Renew Regional Security Push
Read More
Analyst Raises Fresh Questions Over Alleged Fake Government Agency Scandal
Read More
Gombe Governor Launches “Unite Against Terror” Campaign
Read More
Gombe Governor Swears In Newly Elected Local Government Chairmen
Read More